Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce ko da Shugaban Ƙasar ya naɗa matarsa, Remi Tinubu, a matsayin Alkalin Alƙalan Najeriya (CJN), ba zai lashe zaben 2027 ba.

Dalung, wanda jigo ne a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya bayyana hakan ne a wata hira da shirin The Morning Brief na Channels Television ranar Laraba.

Ya ce sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Osun na baya-bayan nan alama ce ta abin da ka iya faruwa a matakin ƙasa.

Ya ce zaɓen Osun ya ƙara tabbatar da hasashen da ya yi tun shekaru biyu da suka gabata cewa Tinubu zai sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ba tare da la’akari da irin naɗe-naɗen da zai iya yi ba.

Dalung ya kuma soki abin da ya kira tara dukiya da jami’an gwamnati ke yi, yana kira ga shugabanni da su fi mayar da hankali wajen gina kyakkyawan tarihi da za a riƙa tunawa da su da shi bayan sun bar mulki.

Ya ce: “Idan muna da shugabannin da ke da lamiri, waɗanda suka san cewa duk waɗannan kuɗaɗen da suke tarawa, wata rana za su bar duniya ba tare da ɗaukar komai ba, za su mayar da hankali wajen gina tarihin da za a riƙa tunawa da su da shi.”

Dalung ya ƙara da cewa ra’ayin yankin zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance sakamakon zaɓen 2027. Haka kuma, ya ce irin yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ta gudanar da mulki da kuma abubuwan da ta cimma za su kasance muhimmin batu a zaɓen.

Duk da haka, Dalung ya dage cewa a ƙarshe za a kayar da Shugaban Ƙasar, yana mai cewa ’yan siyasa da gwamnoni da suka koma jam’iyyar mai mulki ba za su iya tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen 2027 ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *