Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’o’in Najeriya da su fi mayar da hankali wajen koyar da ƙwarewar aiki da kirkire-kirkire da iya magance matsaloli, maimakon mayar da hankali sosai kan bayar da takardun shaidar kammala karatu.
Tinubu ya ce hakan ya zama dole domin ta hakane jami’o’in Najeriya za su samar da ɗaliban da za su iya taimakawa wajen sauya tattalin arzikin ƙasa tare da yin gogayya yadda ya kamata a cikin tattalin arzikin duniya da ke sauyawa cikin sauri.
Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Ilorin, Jihar Kwara, yayin taron shekara-shekara karo na 37 da Babban Taron Kwamitin Mataimakan Shugabannin Jami’o’in Najeriya (CVCNU) ya gudanar a Jami’ar Ilorin.
- Majalisar zartaswa ta amince a sanya kudaden da EFCC ta kwato zuwa bangaren ilimi
- Wasu mahara sun farmaki ayarin motocin gwamnan jihar Osun
- 2027: Ko Tinubu ya naɗa matarsa CJN, ba zai ci zabe ba–Dalung
- Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, wanda Minista a ma’aikatar Ilimi, Suwaibat Ahmad ta wakilta, ya bayyana jami’o’i a matsayin muhimman cibiyoyi wajen ci gaban ƙasa, yana mai cewa aikinsu ya fi bayar da digiri kawai.
A cewar Shugaban Ƙasa, ya kamata a auna ingancin ɗaliban da jami’o’i ke samarwa ta yadda suke iya amfani da ilimin da suka koya da samar da hanyoyin magance matsaloli da kuma bayar da gudummawa mai ma’ana ga al’umma.
Ya ce ana sa ran ɗaliban da suka kammala jami’a za su kasance ƙwararru a fannin ilimi, tare da mallakar wasu ƙwarewa kamar ƙwarewar amfani da fasahar zamani, kasuwanci, iya daidaitawa da sauye-sauye.
Tinubu ya kuma yi kira da a ƙara mayar da hankali kan horon aikace-aikace, yana mai cewa ya kamata ɗalibai su samu damar haɗa ilimin aji da ƙwarewar da ake samu ta hanyar gudanar da ayyuka a zahiri.
Shugaban ya kuma ƙalubalanci shugabannin jami’o’i da su sake duba yadda ilimin da suke bayarwa ya dace da buƙatun sabbin fasahohi.