Ƙungiyar Galatasaray dake buga Gasar Super Lig ta ƙasar Turkiyya, ta yi fatali da tayin yuro miliyan 150 da ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta yi wa ɗan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen.
Ƙungiyar ta Saudiyya ta nuna sha’awar sayan ɗan wasan gaban na Najeriya, wanda aka saya daga Napoli a farkon kakar da ta gabata.
Wata tawaga daga Al-Hilal ƙarƙashin jagorancin yarima Nawaf Bin Saad ta gabatar da tayin. Yariman ya gabatarwa Galatasaray da tayin yuro miliyan 130 akan Osimhen, kuma ya sanar da shugabannin ƙungiyar cewa zai zo birnin Istanbul da kansa idan cinikin zai kasance a hukumance.
-
Gasar Super Six: Yadda Plateau United da Mighty Jets suka yi nasara a wasan farko
-
Julián Álvarez ya shirya kakar wasa ta uku a Atlético Madrid
-
Daga Najeriya zuwa Kamaru: Jerin cikakkun zakarun WAFCON
Al-Hilal ta kuma sanya wa Osimhen kuɗi yuro miliyan 50 a matsayin albashi a kowace shekara. Amma Galatasaray ta sanar da su cewa ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan. Bayan haka, Al-Hilal suka ƙara tayin zuwa yuro miliyan 150.
Duk da wannan babban kuɗin, shugaban ƙungiyar Galatasaray, Dursun Özbek, da kwamitinsa sun yi fatali da tayin gaba ɗaya, inda suka sanar da Al-Hilal cewa sun ƙuduri aniyar riƙe ɗan wasan a cikin ƙungiyar.
Har ila yau, Osimhen da kansa ya bayyana cewa yana cikin farin ciki sosai a ƙungiyar, kuma zai mayar da hankaline kan sabuwar kaka kawai, inda ya sake jaddada cewa kuɗi ba shi ne abin da ya fi bai wa fifiko ba.
Ɗan wasan gaban na Najeriya a halin yanzu, ya zura ƙwallo 2 a wasan farko na kakar bana a kan Çorum FK.
