José Mourinho ya fara kakar wasan bana da kafar dama bayan dawowarsa ta biyu a matsayin kocin Real Madrid, bayan ƙungiyar ta doke Espanyol da ci 2–1 a wasan farko na La Liga na kakar 2026/27.
Jude Bellingham ne ya fara jefa wa Real Madrid kwallo daya, kafin Espanyol ta rama. Sai dai a ƙarshen wasan, Carlos Espí ya zura ƙwallon da ta bai wa Madrid maki uku, inda ya zama gwarzon da ya kawo nasarar a wasan farko na Mourinho bayan dawowarsa Santiago Bernabéu.
- Ajayi ya kawo ƙarshen jiran Hull City na shekaru 9 ba tare da cin ƙwallo ba
- Hull City ta kafa tarihi, ta doke Manchester United bayan shekaru 52
Nasara ce mai muhimmanci ga Mourinho, wanda ya dawo Real Madrid bayan shekaru 13, kuma yanzu zai fara aikinsa na dawo da ƙungiyar saman teburin La Liga bayan Real Madrid ta kammala kakar da ta gabata ba tare da manyan kofuna ba.