Wata kotun birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar ta bayar da belin dan jarida Gazali Abdou Tasaoua, bayan ya shafe tsawon watanmni uku da rabi a tsare.
An dai tsare Tasaoua ne sakamakon wani rahoto da ya yi wanda bai yi wa mahukuntan kasar dadi ba, game da wasu ‘yan ci-rani da ‘yan gudun hijrar Najeriya dake zaman jiran a dawo da su gida a manyan titunan birnin Yamai.
A tsakiyar watan Fabrairun bana ne ‘yan gudun hijrar suka yi wata zanga-zanga a babban birnin kasar ta Nijar, domin nuna rashin gamsuwa da tarwatsa su da aka yi a wani matsuguni da suka yi sansani, lamarin da ya sa daga bisani suka koma wata makabarta suka tare.
‘Yan gudun hijrar sun zargi shugabannin kasashen biyu da tozarta su ta hanyar yin wasarare da rayuwarsu da ta ‘ya’yansu, a halin tsananin bukatar da suke ciki.
A kan wannan al’amari Gazali Abdou Tasaoua ya shirya wani rahoto wanda mahukunta a Nijar ke ganin zai iya haifar da tsamin dangantaka a tsakanin kasashen biyu.
Rahotanni daga Yamai na nuni da cewa yanzu haka dan jaridar ya koma cikin iyalansa, domin ci gaba da rayuwa.
‘Yan jarida da dama kan fuskanci kalubale daga hukumomi bisa rahotanni ko labaran da sukan bayar.
A wasu lokutan har tserewa zuwa wasu kasashe ‘yan jarida kan yi domin guje wa cin zarafi.
