Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce gurɓatar iska na haddasa mutuwar mutane kusan miliyan bakwai a kowace shekara, sakamakon cututtuka da suka haɗa da kansar huhu da cutuka masu alaka ta hanyoyin numfashi da na zuciya.
WHO ta kuma ce kusan mutum tara cikin goma a duniya na shakar iska mai ɗauke da gurɓatattun sinadarai masu lahani ga lafiya.
Rahotanni sun nuna cewa gurɓatcciyar iskar ta fi shafar mata, kananan yara da tsofaffi. Haka kuma, masu juna biyu da jarirai, da kuma tattalin arziki da muhalli.
Sai dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ana iya kauce wa irin wannan ta hanyoyin da za a iya amfani da su wajen magance matsalar.
A bikin na bana, ya fi mayar da hankali ne kan amfanin tattalin arziki da ake samu ta hanyar ɗaukar matakan kare yanayi da inganta iska a lokaci guda.
Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNEP) da ƙungiyar Climate and Clean Air Coalition sun fitar da wani rahoto mai suna Hidden Assets, wanda ya nuna cewa saka hannun jari wajen rage gurɓatar iska da sauyin yanayi na iya samar da ribar tattalin arziki fiye da kuɗin da ake kashewa wajen aiwatar da matakan.
A bikin na bana itama Hukumar kula da yanayi ta Duniya (WMO) za ta fitar da mujallar da ta shafi yadda aka nazarci yanayin yadda Iska ta gurɓatar a shekarar 2025.
Cikin mujallar akwai illar da hayakin daji ya haifar da mummunar illa ga makarin sararin samaniya dake taimakawa duniya daidaita zafin rana wato ozone.
Haka kuma, Majalisar Ɗinkin Duniya za ta gudanar da wani taro ta intanet kan rawar da kamfanoni za su taka wajen yaƙi da gurɓatar iska da kuma tabbatar da cewa kowa na da damar samun iska mai tsafta.
Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ware ranar 7 ga watan Satumbar a kowacce shekara a matsayin ranar wayar da kai game da yaki da illar gurbatacciyar iska ga lafiyar muhalli da dan-adam, tun a shekarar 2020.