Hankulan mazauna Yankin Birnin Tarayya (FCT) da sauran ’yan Najeriya masu bin hanyar Abuja zuwa Kaduna suna kara tashi bayan da aka bayar da labarin mutuwar wani tsohon dan Majalisar Wakilai daga Jihar Jigawa, Honorebul Abba Anas Adamu, a yankin.
Wannan ne dai lamari na baya-bayan nan na satar mutane a kan hanyar wadda ta hade Arewacin Najeriya da birnin na Abuja.
Wani direba mai yawan bin hanyar ya shaida wa jaridar intante ta Premium Times cewa a da hankalinsu a kwance suke bin hanyar, amma a yanzu suna cikin fargaba.
- ‘Muna shirin mayar da Abuja cibiyar kudin bai-daya na Afirka’
- An dakatar da bayar da bizar Amurka a Abuja
- Matsalar Arewa za ta shafi Najeriya –Zainab Buba Galadima
“Mun dade muna bin hanyar hankalinmu kwance babu fargaba musamman da rana; amma a baya-bayan nan sai muka fara samun rahotannin hare-hare a kusa da Jere da wasu wurare ihunka-banza.
“Wani lokaci mutane kan sha da kyar, wani lokaci kuma akan shiga daji da wasu”, inji direban, wanda bai so a ambaci sunansa ba.
Yadda aka ‘kashe’ Honorebul Abba
An ce ranar Laraba aka sace Honorebul Abba Anas Adamu, wanda ke kan hanyarsa ta halartar wani taron jam’iyyar ADC a Abuja daga Kano.
Kwana kadan bayan haka ne kuma aka bayar da rahoton mutuwar tsohon dan majalisar, wanda kusa ne na jam’iyyar ta ADC, a hannun ’yan bindigar da suka sace shi duk da kudin fansar da suka karba.
Rahotanni sun ce an sace Honorebul Abba ne a kusa da Jere tare da wani abokin aikinsa Ali Tukur, sannan aka bukaci a biya kudin fansa Naira miliyan 200.
Sai dai kuma, a cewar wadanda suke da masaniya game da faruwar lamarin, bayan an yi ciniki da ’yan bindigar Naira miliyan 50 aka biya, inda suka saki Ali Tukur.
An dai ce da ma shi Honorebul Abba, wanda ya wakilici mazabar Guri da Kiri-Kasamma da Birniwa a Majalisar Wakilai, yana fama da larurar asma, kuma hana shi samun magani ne ya yi sanadin mutuwarsa a hannun bata-garin.
Shiga da alwala…
Hanyar ta Abuja zuwa Kaduna ta yi kaurin suna wajen tare mutane da yi musu fashi ko ma sace su, kai har ma da kisa a shekarun 2020 zuwa 2022.
Kamarin da satar mutane ta yi a wancan lokacin ya sa matafiya da dama, ciki har da ma’aikata da ’yan kasuwa da manyan jami’an gwamnati da ma ’yan siyasa suka kaurace mata suka koma bin jirgin kasa.
Sai dai layin dogon ma ya fuskanci barazana a 2022, lokacin da aka kai mishi hari, lamarin da ya sa wani jirgin kasa ya fadi, ya bayar da dama aka yi awon gaba da mutane da dama.
Wannan ne ya sa Gwamnatin Tarayya ta tsaurara matakan tsaro a hanyar ta Abuja zuwa Kaduna, lamarin da ya sa hare-hare suka yi sauki matuka.
Amma alamu suna nuna cewa bata-gari sun fara komawa hanyar don ci gaba da cin karensu ba babbaka.
Nesa ta zo kusa…
Jaridar intanet ta Premium Times ta ambato mazanuna kauyukan Rijana da Katari sun bayar da rahoton jin labarin satar mutane da karbar kudin fansa a hanyar.
“Muna jin kishin-kishin game da wadannan labarai domin ba kowa ne yake bayyana abin da ya faru da danginsa a bainar jama’a ba; wasu sukan yi yrajejeniya [da ’yan fashin dajin] su biya kudin fans aba tare da sun sanar da hukumomi ba saboda suna fargabar abin da ka iya faruwa ga ’yan uwansu da aka kama”, wani mazaunin yankin ya shaida wa jaridar.
A yanzu dai babu wanda za ice ga dalilin dawowar sace-sace a hanyar ta Abuja zuwa Kaduna.
Wani jami’in tsaro da Premium Times ta yi hira da shi ya tabbatar da cewa ana ci gaba da sintiri a hanyar.
