Hare-haren mayakan Houthi daga Yemen sun jikkata fararen hula 13 a Saudiyya, yayin da hukumomi suka bayar da gargadin kai hare-hare a birane da dama a safiyar Talata.

Kungiyar Houthi mai samun goyon bayan Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami kan fararen hula a biranen Khamis Mushayt, Abha da Taif, da jirage marasa matuka a ranar Litinin.

Kakakin rundunar hadin gwiwa mai yaki da Houthi a Yemen, Manjo Janar Turki Al-Malki, ya ce hare-haren sun jikkata fararen hula 13 da raunuka daga kanana zuwa matsakaita, tare da lalata gidaje bakwai da motoci biyu.

Al-Malki ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a kafafen sada zumunta da sanyin safiyar Talata.

A nata bangaren, Hukumar Kare Fararen Hula ta Saudiyya ta bayar da gargadin kai hare-hare ga mazauna birane da dama a yammaci da kudancin kasar, ciki har da Abha, Jeddah, Jazan, Taif, Yanbu da Al’Ula.

A ranar Juma’a kuma, Saudiyya ta dakatar na wani aikin shimfida bututun mai na dan lokaci a Riyadh da Madina, bayan wasu jerin hare hare.

Mayakan Houthi na matsa kaimin a yankuna da ake hakar danyen mai a kasar Saudiyya, biyo bayan tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *