Babban Kocin Super Eagles ta Najeriya, Éric Chelle ya Sanya sunan Kyaftin Wilfred Ndidi, da mai tsaron raga Stanley Nwabali, da mai tsaron gida Semi Ajayi, da dan wasan tsakiya Alex Iwobi, da ‘yan wasan gaba Victor Osimhen, da Ademola Lookman da Moses Simon a cikin jerin ‘yan wasa 24 da ya zaba don wasannin neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta 2027 da za a yi da kasar Madagascar da kuma Guinea Bissau, duka a cikin kwanaki 12 masu zuwa.
Super Eagles za ta karɓi baƙuncin Barea ta Madagascar a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo a ranar Juma’a, 25 ga Satumba, kafin ta tashi zuwa Bissau don karawa da Wild Dogs a wasa na biyu a ranar Talata, 29 ga Satumba.
Ga cikakken jerin sunayen ‘yan wasa 24 na Super Eagles da aka gayyata don fafata wasan neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin AFCON ta 2027:
-
Yadda Najeriya ta cire Ingila a Gasar Cin Kofin Duniya ta mata
-
Messi zai sake buga wa Argentina wasa kafin yin bankwanan ƙarshe
-
Taron NFF: Tawagar FIFA da CAF ta kammala tattara bayanai ta koma Zurich
Masu Tsaron Raga: Arthur Okonkwo (Charlton Athletic, England); da Maduka Okoye (Udinese Calcio, Italy); da kuma Stanley Nwabali (Chippa United, South Africa).
Masu Tsaron Gida: Bruno Onyemaechi (Olympiakos, Greece); da Isaac James (Alverca FC, Portugal); da Benjamin Fredricks (Brentford FC, England); da Emmanuel Fernandez (Glasgow Rangers, Scotland); da Oluwasemilogo Ajayi (Hull City, England); da Calvin Bassey (Fulham FC, England); da Chibuike Nwaiwu (Trabzonspor FC, Turkey); da Bright Osayi-Samuel (Birmingham FC, England); da kuma Olaoluwa Aina (Nottingham Forest, England).
‘Yan Wasan Tsakiya: Wilfred Ndidi (Besiktas FC, Turkey); da Alex Iwobi (Fulham FC, England); da Raphael Onyedika (Eintracht Frankfurt, Germany); da kuma Frank Onyeka (Coventry City, England).
‘Yan Wasan Gaba: Moses Simon (Paris FC, France); da Victor Osimhen (Galatasaray FC, Turkey); da Akor Adams (Venezia FC, Italy); da Samuel Chukwueze (AC Milan, Italy); da Ademola Lookman (Atletico Madrid, Spain); da Tolu Arokodare (Ajax FC, The Netherlands); da George Ilhenikina (Al Ittihad, Saudi Arabia); da kuma Moses Usor (LASK FC, Austria).