Wasu majiyoyi sun ce Amurka ta ki bai wa shugaban Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, takardar izinin shiga kasar domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya.

Majiyoyin Sudan da na kasashen Yamma sun ce Washington ta danganta bayar da visa ga amincewar al-Burhan da tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki 90.

Janar al-Burhan ya taba yin jawabi a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya sau biyu tun bayan barkewar yakin Sudan.

Wani mai magana da yawun Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce yana matukar damuwa da cewa har yanzu ba a bai wa al-Burhan visa ba, yana mai cewa suna tattaunawa da Washington kan batun.

Wata majiya ta ce hana shi izinin shiga kasar ya sabawa yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta kulla da Amurka.

Rikicin visa din ya zo ne a daidai lokacin da dangantakar Washington da Khartoum ke kara tabarbarewa, yayin da ake kokarin kawo karshen yakin Sudan, lamarin da ka iya kara tsananta rashin jituwar da ke tsakaninsu.

Rahotanni sun ce akwai yiwuwar Ministan Harkokin Wajen Sudan ya gabatar da jawabi a Majalisar Dinkin Duniya a madadin Janar al-Burhan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *