Gwamnatin Saudiyya ta sanar da samun nasarar haihuwar wani nau’in alfadari a karo na farko a cikin shekaru fiye da dari da samun irinsa a yankin Larabawa.
Hukumar raya Gandun Dajin “Yarima Mohammed bn Salman Royal Reserve” ce ta bayyana hakan. Ta ce an sami haihuwar jaririn alfadarin dajin ne tun a watan Yunin shekarar 2025.
Hukumar raya Gandun Dajin ta bayyana cewa ta dakatar da bayyana labarin ne har sai da jaririn dabbar ya cika shekara guda cif da haihuwa cikin koshin lafiya. Wanda a kimiyance shekarar farko ita ce mafi hadari ga rayuwar ire-iren sa, da rabin su ke mutuwa kafin girma.
Gandun Dajin na Yariman Bn Salman ya bijiro da wani shiri na farfado da namun daji da kuma dawo da nau’ikan dabbobi 23, da ke fuskantar barazanar bacewa zuwa muhallansu na asali.
Hukumar raya Gandun Dajin ta bayyana cewa tana tsammanin samun karin haihuwar wasu alfadarun guda biyu a lokacin hunturun wannan shekara, bayan shigo da wata tamatar alfadara daga kasar Jordan.
Wannan haihuwa ta zo ne a daidai lokacin da Kungiyar Kula da Muhalli ta Duniya (IUCN) ta yi gargadin cewa adadin wadannan dabbobi na iya raguwa da kashi 90% nan da shekarar 2050.
Rahonni na nuni da cewa kasa da guda 600 ne kacal na irin wadan nan alfadarai suka rage a raye a fadin duniya, lamarin da ya sa aka sanya su cikin rukunin dabbobin da ke dab da karewa baki daya.
