Ga mace mai nakuda, wasu lokuta ƴan mintuna kaɗan ne ke iya bambanta tsakanin samun lafiya da fuskantar haɗarin rasa rai.

Zubar da jini mai yawa da hawan jini mai tsanani da haihuwa mai wahala da sauran matsalolin da ka iya tasowa yayin haihuwa na iya rikidewa zuwa yanayin gaggawa cikin ɗan lokaci.

Idan ba a samu kulawar da ta dace cikin lokaci ba, abin da ya fara a matsayin haihuwa ta yau da kullum na iya zama barazana ga rayuwar uwa.

A Najeriya, wannan na ci gaba da zama babbar matsalar lafiyar jama’a.

Bayanan Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta nuna cewa adadin mace-macen mata masu juna biyu da masu haihuwa a Najeriya ya kai kusan 1,000 daga mata 100,000 da suka haihu a shekarar 2023.

Asusun Kula Da Kananan Yara ta Majalisar Dinkion Duniya, UNICEF,  kuma ya bayar da ƙiyasin 993 mace-mace daga mata 100,000 da suka haihu a wannan shekarar.

Wannan adadi ya haifar da cikas da burin Majalisar Ɗinkin Duniya na rage mace-macen mata masu juna biyu zuwa ƙasa da kashi 70 cikin 100,000 kafin shekarar 2030.

Ga wasu mata, matsalar na farawa tun kafin lokacin haihuwa. Wata jami’ar unguwar-zoma, Saudat Abubakar ta ce “Nisan asibiti da kuɗin sufuri da talauci da rashin samun isasshiyar kulawa  lokacin juna biyu da ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan lafiya na iya hana mace samun kulawar da ta dace cikin lokaci”.

A wasu lokuta kuma, ta ce “mace na iya isa asibiti amma ta ci gaba da fuskantar haɗari saboda rashin jini da rashin magunguna ko kayan aiki da rashin ƙwararren likita ko kuma rashin ingantaccen tsarin tura marasa lafiya daga wata cibiyar lafiya zuwa wata”.

Masana kan rarraba wannan matsala zuwa jinkiri guda uku: jinkirin yanke shawarar neman taimakon lafiya da jinkirin isa cibiyar lafiya da kuma jinkirin samun kulawar da ta dace bayan isa asibiti.

Rashin jini na iya zama batun rayuwa da mutuwa

Zubar da jini mai yawa na daga cikin matsalolin da ke buƙatar kulawar gaggawa.

WHO Nigeria ta ba da misalin wata mata da ta fuskanci matsanancin zubar jini makonni bayan an yi mata tiyatar haihuwa, inda iyalanta suka shiga neman jinin da ya dace kafin a iya yi mata tiyatar gaggawa. Daga baya ta tsira bayan an samu jinin.

Wannan ya nuna cewa samun asibiti kaɗai bai wadatar ba; abin da ya fi muhimmanci shi ne ko kayan aikin da ake buƙata wajen ceto rai suna nan a lokacin da ake buƙatarsu.

Shin yawan cibiyoyin lafiya ya isa?

Najeriya tana da dubban cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, kuma bayanan UNICEF sun nuna cewa cibiyoyin sun kai kusan 34,000. Sai dai yawan cibiyoyin lafiya kaɗai ba ya tabbatar da cewa mata za su samu kulawar gaggawa.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne ko mace za ta samu ma’aikatan lafiya da suka ƙware da magunguna da jini da kayan aiki da sabis ɗin haihuwa mai aminci da kuma tsarin tura marasa lafiya da ke aiki yadda ya kamata.

Wani hali ake ciki, wa yake da alhaki?

Idan gwamnati ta ware kuɗi don lafiyar mata masu juna biyu ina kuɗin yake zuwa? Idan an ce asibiti na ba da kulawar haihuwa ta gaggawa, shin kayan aikin suna aiki? Idan an samar da motar asibiti, shin tana nan a lokacin da ake buƙatar ta? Idan mace na buƙatar jini cikin gaggawa, tsawon wane lokaci ake ɗauka kafin a same shi?

Waɗannan tambayoyi ne za su iya sauya labarin mace-macen mata daga rahoton alkaluma kawai zuwa labarin da ke neman alhaki da mafita.

Me ya kamata a yi?

Rage mace-macen mata masu juna biyu na buƙatar ƙarin ma’aikatan lafiya da magunguna da kayan aiki da ingantaccen tsarin tura marasa lafiya. Haka kuma ana buƙatar inganta tsarin samar da jini da sufuri na gaggawa, tare da tabbatar da gaskiya da sahihancin yadda ake kashe kuɗaɗen lafiyar mata.

A ƙarshe, tambayar da ya kamata a yi ba ita ce kawai “mata nawa ne suka mutu ba”?

Tambayar ita ce: “Shin mace ta samu damar isa asibiti cikin lokaci? Shin an samu jinin da take buƙata? Shin magunguna da kayan aiki suna nan? Shin tsarin tura marasa lafiya ya yi aiki? Idan wani abu ya gaza, wa ke da alhakin gyara sh”i?

 

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *