Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun kama sama da mutane 100 da ake zargin an shigo da su domin su kada kuri’a a zaɓen gwamnan jihar Osun da ake gudanarwa yau, Asabar.

An ce mutanen, waɗanda ke ɗauke da sabbin katunan zaɓe na dindindin (PVC), an boye su a gidan wani ɗan jam’iyyar Accord Party mai suna Hon. Abiola Ibrahim, gabanin fara zaɓen.

Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda jami’an tsaro ke yi wa waɗanda aka kama tambayoyi kan dalilin kasancewarsu a wurin da kuma manufar zuwansu jihar.

A yayin tambayoyin, an rawaito cewa Abiola Ibrahim ya amince cewa an mutanen ne a gidansa domin su kada kuri’a ga jam’iyyar Accord Party a zaɓen.

Rahotanni sun ce Ibrahim ɗan Majalisar Dokokin Jihar Osun ne mai wakiltar mazabar Irewole-Isokan.

Sai dai har zuwa lokacin fitar rahoton, ba a samu wata sanarwa daga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun da ta tabbatar ko ta yi karin bayani kan kama mutanen ba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *