A yau ne al’ umar jahar Osun, a Kudu-maso-yammacin Najeriya ke turruruwa zuwa rumfunan zabe a fadin jihar don zaben gwamna.

Ana sa ran masu kada kuri’a sama da miliyan 2 ne za su zai sabon gwamna a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa tuni aka fara tantance masu zabe a runfunan da za au kada kuri’a.

Tuni Babban Sufeton ‘yan sanda na kasa, ya ce an tura isassun jami’an ‘yansanda don tabbatar da tsaro yayin zabe.

An ruwaito cewa an ga jami’an tsaron a wurare da dama a fadin jihar.

Ya zuwa yanzu, an ruwaito cewa babu wata matsala ta tsaro ko wani abu makamancin haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *