Tashar Blueprint Radio ta fara shirye-shiryen gwaji ga Yankin Birnin Tarayya (FCT) a kan mita 105.3 a Zangon FM.
Wannan mataki yana cikin shirye-shiryen da tashar ke yi domin tabbatar da ingancin sauti da tsarin shirye-shirye kafin a kaddamar da ita a hukumance.
A cewar hukumar gudarwar tashar, Blueprint Radio za ta kasance kafar sahihan labarai da tattaunawa da nishaɗi, tare da mayar da hankali a kan al’adu da ci gaban ƙasa.
- Kare ‘yancin ‘yan jarida hakki ne a wuyan mu –Ministan Yada Labarai
- Fitattun ’yan Majalisar Wakilai da suka rasa tikitin APC
- Gaskiya a sadarwa tsakanin gwamnati da talakawa wajibi ce
“Babban makasudin kafa Blueprint Radio shi ne cike wagegen gibin da ake da shi na sahihan labarai a bisa ma’aunin ingnacin da aka amince da shi a matakin kasa-da-lasa a kafafen yada labaranmu, tare da la’akari da ci gaban zamani”, inji shugaban gidan rediyon, Muhammad Kabir Muhammad.
Shirye-shiryen na gwaji dai za su bayar da damar gano matsaloli da gyara su, domin tabbatar da cewa tashar ta fara aiki da cikakken inganci.
Masu sauraro sun fara jin sautin tashar a wasu sassa na Abuja da kewaye.
Wannan ci gaba ya nuna yadda kamfanin Blueprint ke ƙara faɗaɗa ayyukansa daga jarida zuwa rediyo, domin biyan bukatun masu karatu da masu sauraro a lokaci guda.
Babban makasudin kafa Blueprint Radio shi ne cike wagegen gibin da ake da shi na sahihan labarai a bisa ma’aunin ingnacin da aka amince da shi a matakin kasa-da-lasa a kafafen yada labaranmu
Tashar Blueprint Radio ta bukaci al’umma, musamman mazauna FCT, da su ci gaba da bibiyar shirye-shiryenta na gwajin, su kuma bayar da ra’ayi kan yadda za a inganta su kafin a kaddamar da cikakken shirin.
Wadanda suke wajen FCT kuma za su iya sauraron tashar kai-tsaye a www.blueprinthausaradio.com.
Za a iya tuntubar dakin yada labaranta kai-tsaye ta lambar waya 0916 149 1884 ko kuma su bayyana ra’ayoyinsu a shafukanta na sada zumunta da muhawara, wato Facebook da X da Instagram da sauran su aa @manhajarrayuwa.
Za kuma a iya tura sako ta manhajarrayuwa@gmail.com don neman Karin bayani.
