Hukumar Kula da Yanayi ta Ghana (GMet) ta bayyana cewa kasar na asarar kusan Dala miliyan 200 a kowace shekara sakamakon ambaliyar ruwa da fari.
Mataimakin Darakta Janar na hukumar (GMet) Mista Ignatius Williams, ya bayyana hakan lokacin da wata tawagar wayar da kan matasa kan yanayi mai suna (Climate Beyond Borders Caravan) ta ziyarci GMet a Accra.
Karkashin wani shiri na Asusun wanzar da zaman lafiya (People Planet and Peace Foundation), kungiyar Matasan ta (CBBC) sun ziyarci hukumar yanayin ta Ghana (GMet) ne domin karfafa mata gwiwa.
Shugaban tawagar mai suna Williams ya ce Ghana na fuskantar ƙaruwa a barazanar sauyin yanayi, wanda ke jawo asarar biliyoyin daloli a kowace shekara tare da haddasa mutuwar daruruwan mutane.
- An bude Sabuwar Tashar Lantarki a Birnin Yamai
- Bayan Shekaru fiye da 100: An haifi wani nau’in alfadari a Saudiyya
- Yadda muka kashe ɗan ta’adda mafi haɗari ga duniya a Najeriya –Amurka
A cewarsa, waɗannan asarori za su ci gaba da ƙaruwa idan ba a ƙarfafa tsarin gargaɗi da kuma matakan inganta juriyar al’umma ga sauyin yanayi ba.
“A watan Yunin shekarar 2015, ambaliyar da ta afku a Accra ta haddasa asarar tattalin arziki mai yawa, ta yi sanadin mutuwar fiye da mutane 200, sannan ta jawo asarar amfanin gona da aka kiyasta ta kai dala miliyan 108.
“Da malalar ruwan Dam ɗin Akosombo a shekarar 2023, an samu mummunar ambaliya wadda ta lalata hanyoyin rayuwar jama’a, ta raba dubban iyalai da matsugunansu, kuma ta haifar da asarar da aka kiyasta ta kai kusan dala miliyan 141.
“A shekarar 2024 kuma, illolin fari da aka rubuta sun shafi manoma 135,822 a kan filayen noma masu fadin hekta 571,745,” in ji shi.
Daraktan Sashen Hasashen Yanayi na Kasar Ghana (GMet) Mista Joseph Portuphy, ya ce an kafa hukumar ne domin samar da ingantattun bayanai na sauyin yanayi cikin lokaci.
A cewarsa, hukumar na aiwatar da wannan aiki ta hanyar tattarawa, sarrafawa da adanawa da kuma yaɗa sahihan bayanan yanayi, domin tallafa wa ci gaban tattalin arziki da zamantakewa domin kare lafiyar jama’a da rage haɗarin bala’o’i.
Hukumomi a Ghana sun mayar da ita hukuma ne a shekarar 2004 lokacin yana a matsayin Sashen kula da yanayi da aka kafa a Shekarar 1937, Shekaru kusan 67 da suka gabata.
Ayyukan ta sun hadar da lura da yanayi, sarrafa bayanai da daidaita su karkashin dokokin da tsarin hukumar kula yanayi ta duniya (WMO).
