Iran ta ce ta yarda ta hau teburin shawarwari da Amurka, inda ta gabatar da sharuddan 10 da take so a tattauna a kai.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ya karbi wadannan bukatu kuma za su iya kasancewa dan-ba a tattaunawar da za a yi.
Ga bukatun na Iran guda 10:
- Gamsasshen tabbaci daga Amurka cewa ba za ta sake kai wa Iran hari ba.
- Bai wa Iran iko da Mshigin Hormuz mai muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.
- Amincewa da hakkin Iran na ci gaba da sarrafa makamshin nukiliya.
- Dage manyan takunkumin da aka kakaba wa tattalin arzikin Iran.
- Janye dakarun Amurka daga Gabas ta Tsakiya.
- Biyan Iran diyyar baranar da aka yi mata a yakin.
- Kawo karshen matakan soji a kan Iran da kawayenta, ciki har da wadanda suke Lebanon.
- Dage takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Iran.
- Dage takunkuman da Hukumar Kula da Makamshin Nukiliya ta Duniya ta kakaba wa Iran.
- Tabbaci daga kasashen duniya cewa za a aiwatar da wadannan sharuddan.
Sai dai manazarta suna ta diga ayar tambaya a kan ko yiwuwar wadannan sharudda sus amu karbuwa idan aka hau teburin shawarwari.