Ukraine ta kai wani gagarumin hari da jirage marasa matuƙa (drones) cikin dare a yankin St. Petersburg na Rasha, inda aka kai hari kan tashar ajiyar mai da kuma wata tashar jiragen ruwa da ke Tekun Baltic.
Wannan na ɗaya daga cikin manyan hare-haren da Ukraine ta kai a cikin ƙasar Rasha, musamman a garin da Shugaba Vladimir Putin ya fito.
Gwamnan yankin Leningrad, Alexander Drozdenko, ya ce jami’an tsaron sararin samaniya sun harbo jiragen sama marasa matuƙa guda 72 a yankin a ranar Asabar.
An ce an gudanar da harin ne daga nisan kusan kilomita 900 daga yankunan da Ukraine ke iko da su, lamarin da ya haddasa tsaiko ga harkokin sufuri da sadarwa a yankin.
- Zanga-zangar ƙyamar baƙi: An farfasa shagunan baƙi da kwashe kaya
- An ciro Mutumin da ya shafe kwanaki Takwas a ƙarƙashin baraguzan gini a Venezuela
- Masu wanzar da zaman lafiya a Somaliya na fuskantar barazana bayan Amurka ta yanke tallafi
Mahukuntan Rasha sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na ɗan lokaci a filin jirgin saman Pulkovo, sannan suka rage aikin hanyoyin sadarwar intanet ta wayar hannu domin dakile tsarin kewayawar jiragen marasa matuƙa.
Gwamnan St. Petersburg, Alexander Beglov, ya ce ɗaya daga cikin jiragen marasa matuƙa ya faɗi a harabar Peterhof Palace, wata tsohuwar fadar tarihi da aka gina a ƙarni na 18, yayin da wani ya bugi tashar ajiyar mai da ke gundumar Kirovsky
Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce an harbo jimillar jiragen sama marasa matuƙa na Ukraine 389 a faɗin ƙasar cikin dare, amma ta tabbatar da cewa hare-haren sun shafi yankin Leningrad
A nasa bangaren, Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya ce dakarun ƙasarsa sun kai hari kan cibiyoyin mai da ke tallafa wa yaƙin Rasha, tare da kai hari kan sansanin sojojin ruwa na Kronstadt da ke St. Petersburg, wanda ya bayyana a matsayin “wani muhimmin wurin soji.”
Babban Hafsan Sojin Ukraine ya ce hare-haren da suka kai sun lalata kusan kashi 42.74 cikin 100 na ƙarfin tace ɗanyen man fetur na Rasha zuwa farkon watan Yuli.
Ya ce an kai hari kan matatun mai takwas a cikin watan da ya gabata, tare da lalata tankunan ajiyar mai sama da 60.
A cewarsa, asarar da ɓangaren masana’antar man fetur ta Rasha ya yi tun daga watan Agustan 2025 ta kai dala biliyan 13.5.
Sai dai wasu masu nazarin harkokin makamashi sun ƙiyasta cewa tasirin hare-haren ya shafi kusan kashi ɗaya bisa uku ne na ƙarfin tace man fetur na Rasha.
Waɗannan hare-hare sun zo ne kwanaki kaɗan bayan wani hari da Rasha ta kai kan Kyiv, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 30.
Haka kuma, jami’an yankin Sumy sun ce aƙalla mutane huɗu sun mutu yayin da 27 suka jikkata bayan sojojin Rasha sun kai hari da bama-baman kan birnin Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine a ranar Juma’a. Sun ƙara da cewa har yanzu akwai mutane da ke maƙale ƙarƙashin ɓaraguzan wani ginin da harin ya rushe.