Manchester United ta cimma yarjejeniya da Chelsea don sayen ɗan wasan tsakiya na Chelsea kuma ɗan asalin ƙasar Brazil, Andrey Santos, kan fam miliyan 50.
An raba yarjejeniyar zuwa biyan fam miliyan 48 tabbatattu da kuma fam miliyan 2 na la’ada.
Sa’annan kuma Chelsea za ta ci gaba da riƙe kashi 10 na duk wani cinikin sayar da ɗan wasan a nan gaba.
A halin yanzu, Santos na shirin yin gwajin lafiya da ƙungiyar ta Red Devils.
Santos ya fuskanci ƙalubalen rashin damar buga wasanni akai-akai a kakar gasar bara kuma yanzu Chelsea ba za ta buga gasar Zakarun Turai ba.
Santos ya koma Chelsea ne daga ƙungiyar Vasco da Gama kuma tun daga nan ne ya ke buga wasa a matsayin ɗan wasan aro a ƙungiyar Nottingham Forest da kuma Strasbourg.
Santos ya buga wasanni 43 ga Chelsea a dukkan gasa a kakar da ta gabata, inda ya zura ƙwallaye 3 kuma ya bayar da tallafin kwallaye 4.
