Lionel Messi, dan wasan Argentina da Inter Miami

Gabannin ɗaya daga cikin wasa mafi muhimmanci ga tarihin rayuwar ƙwallon ƙafarsa, Lionel Messi ya wallafa saƙo mai ratsa zuciya ga abokan wasansa na Argentina a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026 da Spaniya.

Messi mai shekaru 39 ya wallafa saƙon ne a shafin Instagram inda ya tunatar da abokan aikin sa a kan tafiyar da ta kawo su zuwa babbar dandalin ƙwallon ƙafa, yayin da ya ce haɗin kansu ya fi lashe kofuna.

Messi ya wallafa saƙon ne tare da hoton tawagar ‘yan wasan wanda ya haɗa da ‘yan wasa da masu horaswa da ma’aikata, inda ya ke nuna muhimmancin haɗin kan tawagar ta Lionel Scaloni.

“Abu mafi kyau a cikin waɗannan shekaru ba kawai yadda muka lashe kofuna ba ne, amma yadda muka kasance cikin haɗin kai.”

“Na gode wa kowane ɗan uwana da masu horaswa da kuma duk ma’aikatar da ke aiki kullum domin ganin wannan tawagar ta ci gaba da zama tamkar iyali ɗaya.”

“Duk a bin da zai faru gobe ba zai canza komai ba, mun riga mun kafa tarihi da ba za a taɓa mantawa ba kuma babu wanda zai iya gogewa.”

Wasan ƙarshe na ranar Lahadi da Spaniya za ta zama karo na uku da Messi zai buga a wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya. Gwarzon Argentinan yana neman lashe kofin duniya na biyu bayan ya jagoranci ƙasarsa ta lashe a Qatar shekaru 4 da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *