Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya (ABU), ta rattaba hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) domin haɗin gwiwa wajen ƙirƙiro da gudanar da shirin digirin a Fannin Gudanar da Ayyukan Hajji (MBA Hajj Operations Management – MBA-HOM)

Mataimakin Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, ne ya sanya hannu a madadin jami’ar, yayin da Shugaban Hukumar NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya sanya hannu a madadin hukumar

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne ta hannun Cibiyar Koyar da Dalibai daga Nesa ta Jami’ar ABU (Distance Learning Centre) da kuma Cibiyar Nazarin Hajji ta Najeriya (Hajj Institute of Nigeria – HIN), a wani ɗan gajeren biki da aka gudanar a Hajj House da ke Abuja ranar Juma’a, 31 ga Yuli, 2026.

Yarjejeniyar na da nufin samar da tsarin haɗin gwiwa wajen tsara gudanarwa da kuma ci gaba da inganta ilimi a fannin gudanar da ayyukan Hajji da Umrah.

A karkashin haɗin gwiwar, ɓangarorin biyu za su haɗa kai wajen tsara manhajar karatu da duba ta lokaci-lokaci, tare da gudanar da kwasa-kwasan ƙwarewa kan harkokin Hajji da Umrah.

Haka kuma, za a gudanar da tarukan ƙwararru da shirye-shiryen horas da manyan jami’ai, da ba wa ɗalibai damar yin aikin horo (internship) da koyon aiki a fili, da gudanar da bincike da kirkire-kirkire, da kuma bunƙasa haɗin gwiwa da masana’antu da cibiyoyin ƙasa da ƙasa.

Bisa yarjejeniyar, Jami’ar ABU za ta ɗauki cikakken alhakin gudanar da harkokin ilimi ta hannun Cibiyar Koyar da Dalibai daga Nesa.

Jami’ar ce za ta nemi kuma ta tabbatar da duk wata amincewa da sahalewar ilimi daga hukumomin da suka dace, ta karɓi ɗaliban da suka cika ka’idoji, ta samar da malamai, ta gudanar da jarabawa, tantance sakamako da kuma bayar da digirin MBA a Fannin Gudanar da Ayyukan Hajji.

Har ila yau, jami’ar za ta kula da harkokin gudanarwar ilimi da tallafa wa ɗalibai tare da tabbatar da bin ƙa’idojin ingancin ilimi.

A nata ɓangaren, NAHCON za ta samar da jagoranci na fasaha a harkokin Hajji da Umrah ta hannun Cibiyar Nazarin Hajji ta Najeriya.

Hukumar za ta zaɓo ƙwararrun ma’aikata da za su yi aikin koyarwa a matsayin malamai na wucin gadi, tare da samar wa ɗalibai damar yin aikin horo da ziyartar wuraren aiki a Najeriya da ƙasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *