Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya caccaki tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar yana mai cewa babu wanda ba shi da abin da fada.
Shugaban Kasar ya bayyana haka ne da maraicen ranar Alhamis yayain da yake jawabi ga Jakadun Sabunta Kyakkyawan Fata (Renewed Hope Ambassadors) a Abuja.
Ko da yake bai ambaci suna ba, Tinubu ya yi suka a kan shirin sayar da kadarorin gwamnati, wanda Atiku ya jagoranta lokacin yana Mataimakin Shugaban Kasa.
- 2027: Wannan karon ne takarata ta karshe –Atiku
- Kotu ta baiwa EFCC umarnin kamo Sadiya Umar Farouq
- Tsadar man jirgi ta ta’azzara a Najeriya
A cewar Shugaban Kasar, “Jagoran [‘’yan adawar] ya kasance Shugaban Hukumar Sayar da Kadarorin Gwamnati ta Najeriya…
“Ya sayar da Kamfanin Sarrafa Karafa dake [Jihar] Delta; yana aiki a yanzu?
“Sun sayar da [Kamfanin Sarrafa Karafa na] Ajaokuta; yana aiki yanzu?
“Sun ma satar da jam’iyyar siyasa wani mutum — mutumin ya ce bai yarda ba”.
‘Tinubu ya ba ni kunya…’
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise ranar Laraba, Atiku Abubakar ya yi kakkausar suka a kan Shugaban Kasa Bola Tinubu, yana mai cewa a rayuwarsa bai taba ganin gwamnati mai munin wannan ba.
“Tinubu ya ba ni kunya; ban yi zaton zai gaza haka ba”, inji Atiku.
A jawabin nasa dai Shugaba Tinubu ya ce ‘’yan adawa ba za su taba razana shi ba, balle ya gudu.
Ya kara da cewa ko sau nawa ya samu dama zai maimaiata abin da yake yi.
Jakadun Kyakkyawan Fata
Jakadun Kyakkyawan Fatan dai sun kai wa Shugaba Tinubu ziyara be a karkashin jagorancin shugabansu Gwamna Hope Uzodunma na Jihar Imo.
Shugaban Kasar ya kuma bukace su da su ci gaba da wayar da kan talakawa game da yunkurin da gwamnati take yi don inganta ayuwarsu ta hanyar sauye-sauyen tattalin arziki.
