Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fara zaɓen gwaji wato (straw poll) domin auna irin goyon bayan da ‘yan takara bakwai dake neman kujerar Sakatare Janar ke da shi kafin zaɓen ƙarshe.
Mata huɗu da Maza uku ne ke neman wannan kujerar,kuma mafi girma a tsarin gudanarwar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Michelle Bachelet yar kasar Chile, da Maria Fernanda Espinosa daga Ecuador, Rafael Grossi daga Argentina, Rebeca Grynspan daga Costa Rica sai Carolyn Rodrigues-Birkett daga Guyana,
Sai kuma ‘yan Takara biyu da suka fito daga nahiyar Afirka Olara Otunnu daga Uganda da tsohon Shugaban Ƙasar Senegal Macky Sall.
Macky Sall, ya Shugabanci kungiyar Tarayyar Afirka, kuma ya shahara a jagorantar harkokin diflomasiyya da ƙoƙarin sasanta rikice-rikice a nahiyar Afirka.
Takarar Macky Sall na ɗaya daga cikin abubuwan da ke daukar hankali, kasancewar an daɗe ba tare da wani ɗan Afirka ya riƙe muƙamin Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniyar ba.
- Gwamnatin gabashin Libya ta haramtawa ƙasashen Afirka huɗu shiga ƙasarta.
-
Ghana ta nemi AU ta ɗauki mataki kan hare-haren kyamar baki a Afirka ta Kudu
Shi kuwa Olara Otunnu gogaggen jami’in diflomasiyya ne, da ya taɓa zama Mataimakin Sakatare Janar kuma wakili na Musamman akan kananan Yara da sasanta rikice-rikice tsakanin waɗanda yaƙi ya ɗaiɗaita.
Masana na ganin idan har ɗan Afirka ya yi nasara, hakan ka iya ƙara wa nahiyar tasiri a harkokin diflomasiyya, wanzar da zaman lafiya da kawo gagarumin cigaba.
A daidai lokacin da ake ci gaba da tantance ‘yan takarar, ana sa ran ƙasashe mambobin Kwamitin Sulhu za su gudanar da ƙuri’un na gwaji kafin su fitar da sunan ɗan takarar da za’a miƙa wa Babban taron Majalisar, domin amincewa a matsayin Sakatare Janar.
Wa’adin António Guterres dake kan falle na biyu na shekaru biyar zai ƙare a ranar 31 ga Disamba, 2026.