Ana sa ran Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, zai gana da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif,  a Saudiyya, kamar yadda wani babban jami’in gwamnatin Turkiyya ya bayyana a ranar Juma’a.

Shehbaz Sharif ya isa birnin Jeddah ranar Alhamis domin fara ziyarar aiki ta kwanaki uku, tare da tawagar da ta haɗa da Babban Kwamandan Rundunar Sojin Pakistan, Field Marshal Syed Asim Munir, ministocin tarayya da sauran manyan jami’ai

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan Tahir Hussain Andrabi ya bayyana cewa Firaiminista Sharif zai tattauna dangantakar ƙasashen biyu, da kuma sabbin abubuwan da ke faruwa a yankin tare da Yarima Mohammed bin Salman yayin wannan ziyara

Ziyarar Sharif da Erdoğan na zuwa ne a lokacin da Gabas ta Tsakiya ke cikin rikicin da ya shafi sauran kasashen duniya, biyo bayan hare-haren ramuwar gayya da Iran ke kaiwa kan kasashen da sansanonin sojin Amurka suke a kasashen Larabawa.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soke hare-haren da aka shirya kai wa Iran a ranar Lahadi, yana mai cewa ƙasashen yankin sun cimma muhimman sharuddan yarjejeniya domin kawo ƙarshen yaƙin da Amurkan ke yi da Iran

A farkon wannan mako ma, Iran ta sanar da cewa ta cimma yarjejeniya da Oman kan hanyar jigilar kayayyaki ta mashigar ruwan Hormuz

Turkiyya, Saudiyya, Pakistan, Qatar da sauran ƙasashen yankin sun kasance cikin tattaunawar diflomasiyya na kawo ƙarshen yaƙin da ya fara a watan Fabrairun 2026, bayan wasu tagwayen hare-hare da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *