Darakta-Janar na Kungiyar Hadin Kai da Ci gaban Arewa (ACI), Dakta Abdullahi Idris, ya yi kira ga al’ummar Arewa da su hada kai wajen yaki da matsalar rashin tsaro.
Dakta Abdullahi Idri ya bayyana cewa rashin tsaro na ci gaba da zama babban kalubale ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar yankin.
Shugaban ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da sakamakon bayan taron kungiyar da ta gabatar a makon da ya gabata inda yace dole ne gwamnati, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, malamai da al’umma su hada kai domin kawo karshen matsalar.
- Yadda Marmoush ya zura ƙwallo biyu yayin da Man City ta doke Atletico
- WAFU B U20: Flying Eagles na fatan rama abinda Burkina Faso ta yi mata —- Maikaba
- WAFCON: Marokko ta doke Afirka ta Kudu 2-1
Ya kuma bukaci a karfafa tsarin gargadin farko da daukar matakin gaggawa a cikin al’ummomi domin dakile hare-haren masu aikata laifuka.
Ya ce yaki da rashin tsaro bai kamata ya ta’allaka kan matakan soji kadai ba, sai an magance talauci, rashin aikin yi da sauran abubuwan da ke haifar da rikici.
Darakta-Janar din ya kuma jaddada muhimmancin ilimi da tallafa wa matasa da mata wajen samar da zaman lafiya mai dorewa.
Ya bayyana cewa ACI za ta ci gaba da hada kan masu ruwa da tsaki wajen samar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaba mai dorewa a Arewacin Nijeriya.
