Dakarun Operation Haɗin Kai sun daƙile wani hari da mayaƙan ISWAP suka kai kan sansanin soji da ke Gajiram, a ƙaramar hukumar Nganzai ta Jihar Borno.

Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na dakarun Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

A cewar Goni, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:20 na dare ranar 10 ga Agusta, 2026, lokacin da ɗimbin mayaƙan ISWAP suka kai farmaki kan sansanin da nufin mamaye matsugunin dakarun.

Ya ƙara da cewa hotunan da na’urorin sa ido suka ɗauka bayan artabun sun tabbatar da cewa wasu daga cikin mayaƙan da suka tsira sun kwashe gawarwaki da kuma wasu daga cikin ƴan uwan su da suka samu raunuka yayin da suke ja da baya.

A ɓangaren dakarun Najeriya kuwa, wasu sojoji sun samu raunuka, bayan da wani bangare na tsaron sansanin ya samu matsala na ɗan lokaci.

Harin da aka kai da makaman RPG ya kuma lalata wasu motocin soji da kayan yaki.

A halin yanzu, ana ci gaba da bincike domin tantance  adadin mayaƙan da aka kashe da kuma barnar da aka yi musu yayin artabun.

Goni ya ce rundunar Operation Haɗin Kai za ta ci gaba da matsa wa mayaƙan ISWAP lamba har sai an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *