Wata kotun hukunta manyan laifuka a Damascus Babban Birnin Syria, ta yanke wa tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad hukuncin kisa, kan laifukan da suka shafi murkushe zanga-zangar da ta fara a Syria a shekarar 2011.

Har ila yau kotun ta yankewa tsohon shugaban hukumar tsaron lardin Deraa Atef Najib makamancin wannan hukunci, bayan samun shugabannin biyu da laifin kisan kai da gangan da kuma azabtarwa.

Kotun ta bayyana cewa laifukan da gwamnatin Assad ta aikata a Deraa sun kai matsayin laifukan cin zarafin bil’adama.

Wannan shari’a ta samo asali ne daga abubuwan da suka faru a Deraa a watan Maris na 2011, lokacin da zanga-zangar juyi-juya hali a kasashen Larabawa wato Arab Spring ta fara yaɗuwa a kasashen Gabas ta Tsakiya.

A wancan lokaci ne, jami’an tsaron gwammnati suka kama wasu matasa bisa zargin  su da rubuta kalaman adawa da gwamnati a bangon wata makaranta dake yankin Deraa.

Lamarin da ya haifar da fushin jama’a, inda mazauna yankin suka fara zanga-zangar neman a saki yaran da kuma neman sauyin gwamnati.

Atef Najib, wanda a lokacin yake jagorantar tsaron yankin Deraa, ya kasance ɗaya daga cikin jami’an da ake danganta su da tsaurara matakan da aka ɗauka kan masu zanga-zangar.

Martanin jami’an tsaro ya yi sanadin mutuwar masu zanga-zanga tare da ƙara rura wutar adawar da ta samo asali daga Deraa.

Daga nan ne zanga-zangar ta bazu zuwa wasu sassan Syria, kuma cikin lokaci ta rikide zuwa zubar da jini da ya jefa ƙasar cikin mummunan yakin basasa na tsawon shekaru.

Sai dai hukuncin ya kuma buɗe wani sabon babi na muhawara kan yadda za a gudanar da shari’ar laifukan yakin Syria da kuma ko sabbin hukumomin ƙasar za su iya tabbatar da adalci ga dubban waɗanda suka sha wahala a cikin shekaru fiye da goma na rikici.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *