Tawagar Super Falcons ta Najeriya da takwararta ta Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu za su fafata a Casablanca ranar Alhamis, a wani muhimmin wasan neman cancantar shiga Gasar cin Kofin Duniya na Mata ta 2027.
Dukkan tawagun biyu na gwagwarmayar ci gaba da kuma fatan samun tikitin shiga gasar ne bayan fitar da su daga Gasar cin Kofin Afirka ta Mata (WAFCON) ta 2026.
An fitar da manyan tawagun biyu na Afirka ne a matakin kwata-fainal, hakan ya sa ba su samu tikitin kai tsaye na shiga Gasar cin Kofin Duniya ta Mata ta 2027 wanda za a gudanar a Brazil ba.
- Dortmund ta ɗaga kofin Emirates akan Arsenal
- Yadda Marmoush ya zura ƙwallo biyu yayin da Man City ta doke Atletico
- Kamaru ta cire Najeriya daga Gasar WAFCON
Afirka ta Kudu ta sha kaye da ci 2-1 a hannun ƙasar Marokko mai masaukin baki, yayin da Kamaru ta yi nasara a kan Najeriya da ci 1-0 mai ban haushi.
Rashin samun nasarar su zuwa wasan kusa da na karshe ya sa duka tawagun biyu sai sun biyo ta doguwar hanya kafin zuwa Brazil.
Tuni dai tawagu huɗun da suka kai wasan kusa da na ƙarshe na WAFCON, wato Marokko, da Aljeriya, da Malawi da kuma Kamaru.
Hakan na nufin sun riga sun samu tikitin shiga Gasar cin Kofin Duniya ta Mata kai tsaye.
Kalubalen da ya kamata ku sani game da wannan wasa na ranar Alhamis:
Duk kasar da ta yi nasara a wasan ranar Alhamis za ta tsallaka zuwa zagaye na gaba domin fafatawa da sauran kasashen nahiyar, yayin da ƙasashe shida za su gwabza don cike gurbin wuraren da suka rage na shiga Gasar cin Kofin Duniya.
Wannan zagayen farko zai tantance tawagun da za su tsallaka zuwa matakin ƙarshe, inda za su haɗu da tawagu huɗun da aka ba su tikitin shiga kai tsaye.
Sannan kuma tawagu shidan da suka kai zagayen karshen, za su kara a tsakanin su, yayin da tawagu ukun da suka yi nasarar cin wasannin su, za su samu gurbin shiga Gasar cin Kofin Duniya ta Mata ta 2027.
A saboda haka, Najeriya da Afirka ta Kudu, wasan ranar Alhamis, shi ne shinge na farko cikin shinge uku da ke tsakanin su da shiga Gasar Duniya da za a gudanar a Brazil.
Babu ɗaya daga cikin tawagun da ta yi tunanin sai ta bi ta wannan hanyar bayan wasan kwata-fainal na WAFCON, amma duk wacce ta samu nasara a Casablanca, za ta samu sabon bege na fatan halartar Gasar Duniya a Brazil.
Tarihin Haduwarsu
Najeriya ta fi samun nasara a wasannin baya-bayan nan da suka buga da Afirka ta Kudu. Ta kasance ba ta sha kaye ba a wasanni uku na ƙarshe da suka buga, inda Super Falcons suka samu nasara sau biyu da kunnen doki sau ɗaya.
Haka kuma Najeriya ita ce ƙasa ɗaya a Afirka da ta samu shiga kowace Gasar cin Kofin Duniya ta Mata tun da aka fara a shekarar 1991.
A gefe guda, Afirka ta Kudu tana ɗaya daga cikin ƙasashe uku da suka taɓa lashe Gasar WAFCON, tare da Najeriya da Equatorial Guinea. Sai dai, gasar ta bana tabbas za ta samar da sabuwar wadda za ta lashe kofin.