Masu sharhi kan wasan kwallon kafa a Najeriya sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta fara daukar matakin ladabtarwa akan wadanda ke da alhakin tabarbarewar wasan kwallon kafa a matakin kasa domin ceto fannin daga rugujewa baki daya.
Masu sharhin sun kuma shawarci Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya (NFF) da cewa lokaci ya yi da za ta fara daukar alhaki kan rashin kokarin da tawagun kasar ke yi a matakin wasannin kasa da kasa ba wai za ta dinga fitowa neman yafiya daga al’ummar Najeriya ba.
Masharhantan sun bayyana hakan ne yayin zantawa ta musamman tare da gidan Rediyon Blueprint da ke birnin tarayya Abuja, kwana ki kadan bayan cire tawagun Najeriya biyu, wato Super Falcons da kuma Flying Eagles daga gasar da suke bugawa na nahiyar Afirka.
A ranar Lahadi, 8 ga watan Augustan 2026 ne Super Falcons ta Najeriya ta sha kaye da ci 1-0 a hannun Kamaru a wasan kwata-fainal na Gasar cin Kofin Mata na Nahiyar Afirka (WAFCON) ta 2026.
Wannan shan kaye ya sanya Najeriya, wadda ta lashe gasar sau 10, ta rasa damar zuwa wasan kusa da na karshe don samun tikitin kai tsaye na zuwa Gasar cin Kofin Duniya na Mata da za a buga a Brazil a 2027.
Har yanzu a wannan rana na Lahadi, 8 ga Agusta, tawagar Flying Eagles ta Najeriya ta sha kaye da ci 4-1 a hannun Young Stallions ta Burkina Faso, a wasan karshe na Gasar WAFU B U20 da suka buka a kasar Ivory Coast.
- Yadda Cristiano Ronaldo ya angwance da Georgina
- Kamaru ta cire Najeriya daga Gasar WAFCON
- Dortmund ta ɗaga kofin Emirates akan Arsenal
Rashin samun nasara a wasan yana nufin cewa ba za su halarci Gasar cin Kofin Nahiyar Afirka na ‘yan kasa da shekaru 20 da kuma Gasar cin Kofin Duniya na 2027 na ‘yan kasa da shekaru 20 wanda za a buga a kasar Azerbaijan ba.
A cewar daya daga cikin masharhartan, Alhassan Muhammad Alhassan, dole ne Hukumar Kwallon Kafa ta NFF, ta gyara kurakuran da suke janyo wa Najeriya koma baya kuma duk wanda ya kasa tabuka abun arziki ya ajiye aikin sa.
“Akwai wani kuskure a tafiyar NFF, Super Eagles ma gaba daya ba su iya zuwa sun wakilci Najeriya a Gasar cin Kofin Duniya ba. Ya kamata a tabbatar da menene matsalar kuma a dauki matakin gyara akai,” in ji shi.
“Duk wanda ya kasa, ya ajiye aikin sa. ‘Yan kasa su kira yi cewa mutumin nan dole ya yi murabus. Shugaban kasa ma ya tilasta ma wannan mutumin sabida ya zama izina ga wanda zai zo ya dauki wannan aikin. Hakan shine zai sa a ga komai ya na tafiya daidai a kasa.”
Har ila yau, Alhassan ya yi zargin cewa rashin cika wa ‘yan wasa alkawura da gwamnati ke yi yana taka muhimmiyar rawa wajen rage kwazon ‘yan wasan.
“Akwai alkawura da dama wanda aka daukar wa ‘yan wasa musamman Super Falcons, wanda suka ci Marokko a wasan karshe na WAFCON, Gwamnatin Tarayya ta yi musu alkawarin ba su wasu kudade da gidaje amma har yau a korafin da ‘yan wasan suka yi kwana daya da fara WAFCON na bana, sai da suka fito suna cewa ba’a cika musu alkawarin da aka yi musu ba.” in ji Alhassan.
“Ta yaya za mu yi tunanin cewa wadannan ‘yan wasan za su samu kwarin gwiwar saka karfin su su ga cewa su ciwa Najeriya abinda ya kamata tunda an je wajen babu kwarin gwiwa”?
A na shi tsokacin, Muhammad Musa Bazza, ya ce lokaci ya yi da Hukumar NFF za ta daina maganan neman a gafarta mata a duk lokacin da aka samu koma baya sabida a cewarsa, a baya Hukumar NFF ta taba neman gafara amma har yanzu ta kasa magance matsalolin ta.
“Lokaci ya yi da za mu daina maimaita maganan neman gafara. NFF ta taɓa neman gafara akan raunin wasannin tawagun mu na ƙasa a wasannin da suka gabata, amma har yanzu irin waɗannan matsaloli na ci gaba da faruwa,” in ji shi.
“Dole ne a san wa nene ya ke da alhakin wannan al’amari. Muna da isassun zakakuran ‘yan wasa da ya kamata mu samu gurbin buga Gasar cin Kofin Duniya.
“A gyara harkan ƙwallon ƙafan Najeriya daga sama, Muna buƙatar a samar da kyakyawan tsari da zai inganta gasar mu na cikin gida.
‘Yan Najeriya na fatan duk wandada za a zaba yayin zaben sabbin shuwagabanni na Hukumar NFF da za ayi a watan gobe, a garin Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa, za su gaggauta magance matsalolin da suka hana harkar kwallon kafa ci gaba a Najeriya.