Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayar da shawarar cewa ya kamata kowane ɗan Najeriya ya samu horon soja domin ya fahimci irin bukatu da sadaukarwar da ake yi wajen kare kasa.
Janar Musa ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin African Leadership Podcast tare da Ken Giami, wanda aka wallafa ranar Litinin.
A cewarsa, horon soji na koya wa mutum yadda ake jure yunwa da gajiya,da wahalar jiki da sauran matsalolin da sojoji ke fuskanta, lamarin da zai ba mutum wata fahimta ta daban game da rayuwa da kuma nauyin kare kasa.
- Ministan tsaro ya jaddada kudirin Najeriya na wanzar da zaman lafiya a duniya
- Katsina ta cika shekaru 39 da kafuwa
- NSCDC ta sake jaddada gaskiya da bin doka yayin binciken mutuwar masu haƙar ma’adinai
Ya ce horon zai taimaka wa mutane su fahimci yadda ake jure yunwa da kuma yin aiki na tsawon kwanaki ba tare da isasshen barci ba.
Janar Musa ya ce sadaukarwar da sojoji ke yi domin kare kasa ta yi kama da ka’idar da ke cikin Littafi Mai Tsarki ta mutum ya sadaukar da ransa domin wani.
Ya ce sojojin Najeriya na jefa rayukansu cikin hadari domin tabbatar da cewa kasar ta samu damar ci gaba da tafiyar da harkokinta cikin tsaro.
Tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su fahimci cewa sojoji ma mutane ne da ke da iyalai, wadanda suke barin iyalansu a gida yayin da suke gudanar da ayyukansu na kasa.