Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) ta ce za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Hukumar NIMC domin wayar da kan al’umma kan muhimmancin yin rajistar Lambar Shaidar Zama Ɗan Ƙasa (NIN).
Darakta Janar na hukumar, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana haka yayin ganawar da jami’an NIMC suka yi da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai a Abuja.
- Gwamnatin Tarayya na ƙara ƙaimi wajen yi wa ‘yan Najeriya rajistar NIN –Minista
- Majalisar Wakilai ta yi fatali da buƙatar gayyato Tinubu
- NIMC ta fara rajistar NIN a mazaɓu 8,809 na ƙasar
Ya ce kasancewar NOA tana da ofisoshi a dukkan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar zai taimaka wajen isar da saƙon gwamnati ga al’ummomin karkara da waɗanda ba su da sauƙin samun bayanai.
Ya ƙara da cewa haɗin gwiwar zai tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya ya fahimci amfanin rajistar NIN kuma ya samu damar cin gajiyar shirye-shiryen gwamnati.