Aljeriya ta kammala Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka na Mata (WAFCON) ta 2026 da ake bugawa a Marokko a matsayi na uku bayan ta doke masu masaukin baƙi da ci 3-2 a bugun fenareti, bayan wasan ya ƙare da ci 1-1 a cikin mintuna 90.

Masu masaukin baƙin sun fara wasan da ƙarfin su, inda bugun Ibtissam Jraidi ya kusan shiga raga a minti na 17.

Daga bisani Marokko ta samu nasarar zura ƙwallo a minti na 26 ta hannun Kautar Azraf a wani yunƙuri mai ban sha’awa.

Azraf ta sake samun damar ƙarin cin wani ƙwallo, amma ƙwallon ta canza alkibla daga baya.

Jraidi ta sake samun wata dama a minti na 63 lokacin da aka tura mata wani ƙwallo inda ta fuskanci mai tsaron ragar, amma ta kasa buga ƙwallon da kyau.

Algeria ta dawo bayan hutun rabin lokaci cikin tsari mai kyau, inda ta matsa wa masu tsaron gidan Marokko lamba tare da samar da damarmaki.

Matsin lambar ya haifar da ɗa mai idanu a minti na 83 bayan Melissa Bethi ta bayar da kyakkyawar ƙwallo daga tsakiya ga Boussaha, wacce cikin kwanciyar hankali ta buga ƙwallon ta wuce cikin raga, inda wasan ya koma ci 1-1.

Babu wata tawaga da ta iya ƙara cin wani ƙwallo har aka tashi a wasan, aka tafi bugun fenareti.

Yayin bugun fenaretin, Aljeriya ta yi nasara da ci 3-2, inda Ines Belloumou ta zura bugun fenareti na ƙarshe da ya tabbatar da nasarar da ba za a manta da ita ba.

Wannan sakamako ya bai wa Aljeriya lambar tagulla da matsayi na uku a Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka na Mata ta 2026, yayin da masu masauƙin baƙi, Marokko suka ƙare a matsayi na hudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *