Hukumar Yanayi WMO tace duniya zata fuskanci sauyin zafi shekaru Biyar a jere

Hukumar Kula da Yanayi ta Duniya (WMO) ta fitar da wani gagarumin gargadi ga al’ummar duniya game da sake dawowar yanayi da zai  haddasa tsananin zafi, fari, da kuma gurbacewar yanayi.

WMO ta yiwa yanayin lakabi da “El Nino” dake haifar da zafi marar misaltuwa sakamakon dumamar da ruwan Teku keyi.

Hukumar ta bayyana cewa halin da Tekun Pacific ke ciki a halin yanzu alama ce mai nuna cewa duniya za ta fuskanci karuwar zafi fiye da kowane lokaci, lamarin da zai iya haifar da fari a wasu yankunan, ko kuma ambaliyar ruwa a wasu.

Sakatariyar hukumar yanayin ta duniya Celeste Saulo ta bayyana cewa, kowace kaka kan zo da kalubale, a wannan karon zaa samu jinkirin faduwar damuna da karancin yawan ruwan saman da ake bukata don noma a wasu sassa.

Yayin da a bangaren lafiya tsananin zafin ka iya haifar da cututtuka irin su zazzabi da matsalolin numfashi.

Saulo ta kuma ce zaa fuskanci raguwar adadin ruwan da ake bukata a madatsun ruwa, don sha da kuma samar da wutar lantarki.

“Wannan ba gargaɗi ba ne na firgita, shawara ce ga gwamnatoci da su gaggauta shiri tun kafin lokaci ya kure domin kare rayuka da tattalin arziki.” — In ji ta.

A karshe Hukumar  ta yi kira ga kasashe da su kafa cibiyoyin gaggawa domin adana abinci da madatsun ruwa, da kuma bai wa manoma shawarwari game da irin  noma mai jure fari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *