A halin yanzu, dan wasan gaban kasar Norway, Erling Haaland ya kamo Kylian Mbappe da Lionel Messi a gasar neman lashe Takalmin Zinare a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.

Dukkanin manyan taurarin suna cigaba da nuna bajinta a fafatawar zama mafi yawan zura kwallaye a gasar da ƙasashen Amurka, Kanada da Mexico ke ɗaukar nauyi.

Haaland ya jagoranci Norway zuwa kwata fainal a karon farko kuma ya karfafa matsayinsa a jerin masu zura ƙwallaye ta hanyar zura kwallo biyu da suka fitar da Brazil.

Yanzu haka Haaland, ya na da kwallaye 7 dai-dai da manyan ƴan wasa irin su Mbappe da Messi.

Kyaftin din England, Harry Kane ne na gaba da kwallaye 6 bayan bugun fanaretin da ya taimaka wa tawagarsa doke mai karbar baƙunci Mexico 3-2 domin fafata wasan kwata fainal da Norway.

Ga yadda jadawalin masu neman lashe Takalmin zinare take a yanzu…

  1. Erling Haaland (Norway) 7
  2. Kylian Mbappe (Faransa) 7
  3. Lionel Messi (Argentina) 7
  4. Harry Kane (Ingila) 6
  5. Ismaila Sarr (Moroko) 4
  6. Jude Bellingham (Ingila) 4
  7. Julián Quiñones (Mexico) 4
  8. Mikel Oyarzabal (Spaniya) 4
  9. Ousmane Dembélé (Faransa) 4
  10. Vinícius Júnior (Brazil) 4

Wa nene kake ganin zai lashe Takalmin Zinaren a karshen karshe?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *