Kimanin mutane goma sha shida ne suka samu raunika bayan da wani gini ya rufta a anguwar Ɗandinshe, kwanar Yashi dake ƙaramar hukumar Fagge ta Jihar Kano.
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa.
Ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 4:32 na asuba daga ɗaya daga cikin ma’aikatanta, Aminu Sani Warure.
- Zamfara: Sojoji sun lalata abin fashewa, sun kama mutane biyu
- Gobarar tankar mai a Abuja: Ma’aikatan kashe gobara uku sun jikkata
- Masu neman karafa sun cire sandunan ƙarfe daga ginshiƙan gada a Legas
Abdullahi ya ce jami’an hukumar sun gaggauta zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka tarar da wani gini mai faɗin ƙafa 20×30 ya rufta tare da danne mazauna cikin sa.
Daga cikin waɗanda suka jikkata akwai Al-Mustapha Yusuf, mai shekaru 15; Khadija Yusuf, mai shekaru 7; Ummusalama Yusuf, mai shekaru 10; Madina Yusuf, mai shekaru 6; Hafsat Yusuf, mai shekaru 9, da wasu mutum takwas waɗanda ba a samu sunayensu nan take ba.
Sai dai Abdullahi yace jami’an hukumar sunyi nasarar ceto wasu mutane Uku da ransu a cikin ɓaraguzan ginin.
Abdullahi ya ce har yanzu ana gudanar da bincike domin gano musabbabin ruftawar ginin.
Ya shawarci mazauna yankin da su ƙara taka-tsantsan a lokacin damina domin kauce wa sake faruwar irin wannan mummunan lamari.